<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>129</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Farkon zuwan Almasihu daga Sama ne ya zo
 Zaman neman duk mutane ƃatattu
 Komawarsa ta yi kusa, ya yi zancen taimako,
 Masu Binsa suna nan, ya ce da su.

[V2]
 KORUS
 &quot;Zuciyarku kar ta ƃaci,
 Sai ku ji, ku gaskata ni.
 Sama za ni gun Ubana,
 Nan zan shirya muku wuri har in zo.&quot;

[V3]
 2) Yesu ya yi zance cewa, &quot;Gidan Ubana 'na nan,
 Wurin zamansa dayawa, sai in je
 Don in shirya muku su, in zo in kai ku wata ran,
 Inda na ke zaune fa a nan ku ke.&quot;
 Korus

[V4]
 3) Sake zuwan Ubangiji mu ke sauraronsa yau.
 Shi alkawarinsa ba zai karya ba.
 Zato babu, ba tsammani, murya tasa za mu ji.
 Mai Cetonmu, ga shi, yana saukowa!
 Korus

[V5]
 4) Kashin tsarkakansa biyu ne, matattu da masu rai.
 Yesu dai zai fara ta da matattu.
 Masu rai fa gaba ɗaya zai fyauce su nandanan,
 Har ya sa su a wurare shiryayyu.
 Korus</lyrics>
<title>Farkon Zuwan Almasihu Daga Sama Ne Ya Zo LW129</title>
<author>Black, James Milton (1856-1938)</author>
</song>